A shirin mu na yau, Barista Umar Isa Suleiman fitaccen lawya a Najeriya, ya bayyana matsayin bangaren shari’a a tsarin dimokradiyyar Najeriya da irin kalubalen da ya ke fuskanta.

 

A wannan shirin, mun tattauna da Dr. Aminu Isma’il Sagagi, malamin jami’a kuma fitaccen mai sharhi kan batun wata hukumar bogi a Najeriya dake janyo cece-kuce.

 

A wannan shirin Alhaji Hamisu Ahmed Uba, Sarkin Kasuwar abinci ta Dawanau dake Kano, ya ce har yanzu, akwai fata a harkar noma duk da matsalar rashin tsaro a wasu sassan Najeriya.

 

A wannan shirin, Alhaji Sa’idu Adhama ya bayyana cewa dole sai an tallafawa masana’antu a Arewa da Kano, muddin ana san bukasa tattalin arzikin yankin.

Tattaunawa da Barista Umar Isa Suleiman, fitaccen lauya a Nigeria, wanda ke sharhi kan yadda ake gudanar da harkokin shari’a a wannan zamani na siyasa a kasar.

Yaya tsarin dimokradiyya da gudanar da mulki ke tafiya yanzu a Nigeria? Hira da Dr Hakeem Baba Ahmed, fitaccen mai fafutukar wanzar da mulki na-gari. 

Dr Saidu Ahmad Dukawa masanin Tarihi da Siyasa na jami’ar Bayero dake Kano ya ce ‘yan Najeriya dole su jajirce wajen kawo gyara a harkokin mulkin kasar. 

Hira da Dr Sadiu Ahmad Dukawa masanin Tarihi da Siyasa na jami’ar Bayero dake Kano kan dangantakar siyasa da tsaro. Ya fara da yin tsokaci a game da halin tsaro yanzu a Nigeria. 

A wannan hirar da Dr. Aliyu Tilde, masanin siyasa a Nigeria, ya ce dole fa, sai an yiwa dokar zabe gyara muddin ana san saita tsarin dimokradiyya a kasar.

Dr Aliyu Tilde masanin tarihi da siyasa daga jihar Bauchi ya fadi yadda za’a samu mafita a tsarin dimokradiyyar Nigeria dake tangal-tangal. 

Tattaunawa da Profesa Kamilu Sani Fagge, masanin mikiyyar siyasa na jami’ar Bayero dake Kano, kan yaya za’a kawo karshen rashin tsaro a Nigeria. 

Sharhi kan tushen matsalar rashin tsaro a Nigeria, da kuma sakamakon da ya haifar a kasar, musamman a yankin Arewa. 

Hira da matashi Abubakar Haruna, mai aikin wutar lantarki, kan mahimmancin dogaro da kai a tsakanin matasan Nigeria. 

A ci gaba da hira da wani dan dabar siyasa, a wannan shiri ya bayyana irin rawar da ‘yan jagaliya suke takawa a ranakun zabe. 

Hira da wani dan daba dake bayyana yadda ‘yan siyasa ke daukar su aiki a matsayin ‘yan banga ko jagaliyar siyasa a manyan birane.  
Tattaunawa da Ambasada Yunusa Yusuf Hamza mai gwagwarmayar yaki da shaye-shaye da fadace-fadace tsakanin matasa a Kano.
Me yasa har yanzu mata ke fuskantar kalubale wajen shiga siyasa a Nigeria? Hira da Dr Asabe Vilita Bashir, tsohuwar ‘yar siyasa daga jihar Borno. 

A wannan shiri na Gaskiyar Magana, mun yi hira da dan Siyasa Hon. Abdullahi D. Dankano, dangane da batun siyasar Ubangida a Nigeria. Ya duba amfani da illolin ta. 

Hira da Profesa Shua’ibu Shehu Aliyu, masanin tarihi da siyasa, kuma tsohon malami a jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria. Ya ba da karin haske kan matsalar da ta zama ruwan dare. 

Menene dalilan da suke sanya jam’iyyun siyasa a Nigeria a kullum suke cikin rikici, duk da tarihin tsahon shekaru sama da 100 da kasar ke siyasa karkashin jam’iyyu? 

Tattaunawa da dan siyasa Hon. Abdullahi Dalhatu Dankano, tsohon sakataren  jam’iyyar CPC na jihar Kano. Ya bayyana kalubalen wannan batu, inda ya ce kowa na da laifi a ciki.

A wanan shiri, mun yi nazari kan yadda ake amfani da kudi a siyasar Nigeria. Me ake nufi da siyasar kudi? Mun duba tasirin da siyasar kudi ke yi bisa tsarin dimokradiyya. 

Tattaunawa da fitaccen masani kan harkokin siyasa Profesa Bello Bada, inda yayi tsokaci kan magudin zabe, da wadanda ke da hannu a lalacewar harkar zabe a Nigeria. 

A wannan shirin mun tattauna da Profesa Bello Bada, masani kan harkokin siyasa da tarihi, dan jin ko a zahiri, hukumar zaben Nigeria (INEC) mai zaman-kan ta ce. 

A cikin wannan shirin mun duba tsarin zaben Nigeria da kalubalen matsalolin dake tattare da tsarin.

A cikin wannan shirin mun duba takaitaccen tarihin tsarin dimokradiyyar Nigeria bayan kasar ta shafe shekaru masu dama a karkashin mulkin soja. 

A cikin wannan tirelar mun nemi masu bibiyar mu, da su kasance da mu, a daidai lokacin da muke shirin kaddamar da sabon shirin na mu.